Kamar Yadda Gwajin HIV Yake Dole Kafin Aure, Haka Ma Na Shan Kwayoyi, Buba Marwa
- Shugaban hukumar NDLEA ya bayyana bukatar yi wa mutane gwajin shan kwayoyi kafin a yi aure
- Ya bayyana haka ne da nufin rage shaye-shaye da ke addabar al'umma Najeriya cikin shekarun nan
- Hakazalika ya bayyana adadin da ake samu na masu shan miyagun kwayoyi a cikin al'ummar Najeriya
Janar Buba Marwa (mai ritaya), shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ya bayyana bukatar gwajin shan miyagun kwayoyi kafin a yi aure kamar yadda ake na HIV.
Buba Marwa ya fadi hakan ne a wata hira da BBC Hausa albarkacin ranar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyo Ta Duniya da ake yi duk ranar 26 ga watan Yunin kowace shekara.
KU KARANTA: Muna Godiya: Ganduje Ya Jinjina Wa Sojoji Bisa Kare Dajin Falgore da Jihar Kano
Yayin da yake zantawa, Marwa ya ce:
"A kasar nan, mutum daya cikin bakwai, yana shaye-shaye. Majalisar dinkin duniya a kowace shekara tana zaban rana daya, wanda duniya za ta hade a yi jawabi kuma a nemi mafita game da shaye-shaye a duniya baki daya.Ya kuma ta'allaka tashe-tashen hankula da yawaitar sace daliban makaranta dake faruwa a kasar da shan miyagun kwayoyi.
Hakazalika, ya ce game da auren dan shaye-shaye:
"Me yasa idan ana gwajin HIV, Genotype kafin a yi aure, me ya hana a yi shan miyagun kwayoyi shima? Dole mu fito da wasu hanyoyi."Barnar Boko Haram da Na 'Yan Bindiga Basu Kai Illar Shan Miyagun Kwayoyi Ba
A gefe guda, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa fataucin miyagun kwayoyi ya haifar da manyan hadurra ga Najeriya fiye da ayyukan 'yan ta'adda mabambanta.
Shugaban na Najeriya ya yi wannan bayani ne a ranar 26 ga Yuni, a yayin kaddamar da shirin yaki da miyagun kwayoyi na WADA, The Nation ta ruwaito.
Buhari, wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Boss Mustapha, ya ce yaki da shan miyagun kwayoyi yaki ne da dole ne a yi shi ba kakkautawa.
KU KARANTA: Shinkafa Ta Wadata a Najeriya, Saura a Fara Fitarwa Kasashen Waje, in Ji RIFAN
NDLEA ta yi nasarar cafke dillalan miyagun ƙwayoyi 231 a jihar Oyo
A wani labarin, Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, reshen jihar Oyo, ta ce ta kama mutane 231 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi daga watan Yunin 2020 zuwa Yunin 2021, Pulse NG ta ruwaito.
Da ya ke yi wa yan jarida jawabin, a ranar Alhamis game da ayyukan da hukumar ta yi cikin lokacin da ake nazari, Josephin Obi, kwamandan jihar ya ce mutum 215 cikin wadanda ake zargin maza ne yayin da 16 kuma mata.
Mrs Obi, wacce ta samu wakilcin mataimakin kwamanda Anthony Gotar ta kuma ce rundunar ta yi nasarar kwace ganyen wiwi mai nauyin 6,355.74 da wasu kayan maye a cikin watanni shida.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHB9k2tpa3BhYriiucCrZLKZlJmubrPWmqGipl2dtrd52JqinmWUpLmmecqanaKmXZbCs7GMoZikmV2irm66wGaqoZmeYri4rdiosKJlkqqvonnMmqmwmV6dwa64